3 Oktoba 2026 - 20:38
Source: ABNA24
Pakistan: Shugabancin Taliban Ne Ke Da Alhakin Yaduwar Ta'addanci Daga Ƙasar Afghanistan

Sojin Pakistan a taron kwamandojin rundunar, sun tabbatar da halaltaccen haƙƙin kare kai da matakin da aka dauka kan ta'addancin da ya samo asali daga Afghanistan kuma sun ɗaurawa shugabancin Taliban da alhakin musabbabin waɗannan matakan a madadin Indiya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Kafofin watsa labarai na sojin Pakistan a cikin wani saƙo sun ce Marshal Syed Asim Munir, shugaban hafsan soji kuma shugaban sojojin tsaro na Pakistan, ya jagoranci taro na 277 na kwamandojin rundunar a hedkwatar babban hafsan soji a Rawalpindi.

A cewar sojin Pakistan, wannan taron da aka gudanar da yammacin jiya Juma'a ya nazarci yanayin tsaron Pakistan na yanzu kuma ya nanata kiyaye cikakken shiri ko ta kwana. Wannan taron ya tabbatar da halattaccen haƙƙin kare kai na Pakistan da gudanar da matakan da aka yi qudirinsu kan yaki da ta'addancin da ya samo asali daga Afghanistan kuma ya bayyana cewa ruɗaɗɗen shugabancin Taliban kaɗai da ke alhakin haifar da ta'addanci a madadin Indiya, kuma shine ke da alhakin sakamakonsa.

A cikin wannan saƙo an bayyana cewa kwamandojin soji sun yaba da nasarar ayyukan yaƙi da ta'addanci da suka dogara kan bayanai, amma sun nanata wajibcin kammala matakan soji da matakan fararen hula ciki har da mulkin da ya dogara kan jama'a a matakin yankin, dangantaka ta dabarun da jama'a, lalata alaƙar ta'addanci da laifi da ƙarfafa 'yan sanda.

Wannan taron ya nanata kwanciyar hankalin cikin gida na sojin Pakistan kuma ya yi gargaɗi cewa duk wani ƙoƙari na haifar da rashin kwanciyar hankali kamar 9 ga Mayu za a murkushe shi da ƙarfi kuma bisa doka. Haka kuma an yi maraba da yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa ta Makka tsakanin Pakistan, Saudiyya da Turkiyya kuma an bayyana haɗin kai ga Saudiyya wajen fuskantar hare-haren Houthiyawa.

Ya kamata anbaci cewa dangantakar Pakistan da Taliban bayan komawar wannan ƙungiyar kan mulki a shekarar 2021 a hankali ta yi tsamari. Islamabad tana tsammanin Taliban za ta hana ayyukan ƙungiyar Tehrik-i-Taliban Pakistan (TTP), amma hare-haren wannan ƙungiyar daga ƙasar Afghanistan kan sojojin tsaro da fararen hular Pakistan sun ƙaru sosai. Pakistan tana zargin Taliban da samar da mafaka da tallafawa TTP; a lokacin da Kabul ke ƙin wannan zargin kuma tana ɗaukar batun a matsayin na cikin gida. Waɗannan sabanin tun shekarar 2025 sun kai ga hare-haren sama na Pakistan kan ƙasar Afghanistan, rikice-rikicen iyaka da ayyana "yaƙi na fili" daga jami'an Islamabad.

..............

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha