(ABNA24.com) Hukumar kula da lamuran makamashin Nukliya a duniya wasu IAEA ta fara tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran, da kuma yarjejeniyar JCPOA ta kafar hotunan bidiyo sanadiyar Cutar Korona.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar, Rafael Mariano Grossi yana fadin haka a jawabin bude taron a jiya Litinin, sannan ya bukaci kasar Iran ta bada dama wa jami’an hukumar su binciki wasu wurare biyu a kasar, wadanta ta sami sabbin bayanai dangane da su
Gwamnatin kasar Iran dai ta bayyana cewa bukatar binciken wurare guda biyu a kasar Iran ta zo ne bayan da Haramtacciyar kasar Isar’ila ta gabatar da takardun shaida na jabu ga hukumar.
Jakadan kasar Iran a hukumar Kazem Gharib ya gargadi shuwagabannin hukumar ta IAEA da kokarin bata kekyawar dangantaka da ke tsakaninta da hukumar. Banda haka ya kara da cewa irin halin da hukumar take nunawa zai kada mutuncinta.
/129
16 Yuni 2020 - 08:26
Lambar labari: 1047188
Hukumar kula da lamuran makamashin Nukliya a duniya wasu IAEA ta fara tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar Iran, da kuma yarjejeniyar JCPOA ta kafar hotunan bidiyo sanadiyar Cutar Korona.