14 Yuni 2020 - 09:15
​Masar Ta Kirayi Kasashen Musulmi Da Su Mara Baya Ga Falastinu

Gwamnatin kasar Masar ta jaddada kira ga kasashen musulmi da su yi sahu guda tare da al’ummar Falastinu domin ba su goyan wajen kare hakkokinsu.

(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Masar ta jaddada kira ga kasashen musulmi da su yi sahu guda tare da al’ummar Falastinu domin ba su goyan wajen kare hakkokinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar Russia Today cewa, Sameh Shukri ministan harkokin wajen kasar Masar ya jadadda cewa babu ja da baya kan batun goyon bayan al’ummar Falastinu.

Ministan harkokin wajen kasar ta Masar ya bayyana hakan ne a zaman gaggawa da kungiyar kasashen musulmi ta OIC tagudanar ta hanayar hotunan yanar gizo, kan batun shirin Isra’ila na mamaye sauran yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

Ya ce batun Falastinu lamari ne da ke bukatar daidaiton baki da daukar matsayi guda daya a tsakanin dukkanin kasashen musulmi, domin su yi magana da harshe daya na kin amincewa da wannan shiri na Isra’ila.

Haka nan kuma ya bukaci sauran kasashen musulmi da su taimaka ma al’ummar Falastinu a cikin wannan mawuyacin hali na bullar cutar corona.

Daga karshe ministan harkokin wajen na Masar ya ce suna goyon bayan matsayar da gwamnatin Falastinawa ta dauka na yin sayin daka kan hakkokin al’ummar Falastinu da kuma yin watsi da shirin na Isar’ila wanda yake a matsayin wani sabon mulkin mallaka a kan al’ummar ta Falastinawa.


/129