(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Faransa ta kaddamar da sabon kawancen sojoji na yankin Sahel wanda zai hada kasashen Afrika da kuma Turai wanda zai bunkata kawancen da ake da ita a kasa don yakar ‘yan ta’adda a yankin sahel na yammacin sahara.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa kasar Faransa za ta gudanar da taro ta kafar bidiyo nan ba da dadewa ba don ministocin tsaro na kasar 45 wadanda zasu shiga cikin sabuwar kawancen wanda ta bayyana labarin samar da shi a cikin watan Jenerun wannan shekara.
A halin yanzu dai gwamnatin kasar Farasansa tana da sosjoji 5,100 a yankin tun shekara 2013, sai dai al’amuran tsaro a yankin ya kara tabarbarewa a shekarar da ta gabata.
A wannan karon dai ana saran kawancen zai sami tallafin sojoji da kayan aiki har’ila yau kasashen kamar Saudia da Hadadiyar daular larabawa zasu taimaka da kudade.
‘Yan ta’adda wadanda suke danganta kansu da kungiyar Alqaeda sun addabi kasashen na Sahal tun shekara 2012. Kasashen dai sun hada da Niger, Mali, Mauritania, Chadi da kuma Burkina Faso.
/129
14 Yuni 2020 - 09:15
Lambar labari: 1046310
Gwamnatin kasar Faransa ta kaddamar da sabon kawancen sojoji na yankin Sahel wanda zai hada kasashen Afrika da kuma Turai wanda zai bunkata kawancen da ake ...