(ABNA24.com) A jawabinsa a wajen bikin bude wasu masana’atu biyu a lardunan Khurasan da Isfahan ta hanyar bidiyo a yau Alhamis: Shugaban kasar Iran Dr Hasan Ruhani ya bayyana cewa duk wani matakin matsin lamba ta hanyar kakaba takunkumi kan Iran, ba zai taba raunana ruhin dogaro da kai da karfin gwiwar al’ummar kasar ba. Yana mai jaddada cewa: Duk da tarin takunkumi da matsi lamba kan kasar ta Iran amma ta samu gagarumin nasarori a fagen dogaro da kanta a bangarori da dama, inda a halin yanzu ta rubanya yawan karafuna da take samarwar idan aka kwatanta da shekarun baya.
Har ila yau Dr Ruhani ya kara jaddada godiya ga Allah Madaukaki kan irin taimakon da yake yi ga al’ummar Iran wajen samun ci gaba a bangarori daban daban, inda Iraniyawa suke taka rawa a fagen ci gaban duniya, kamar yadda ya kara karfafa Iraniyawan kan kara kokari domin ciyar da kasarsu gaba.
/129
13 Yuni 2020 - 09:57
Lambar labari: 1045852
Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Cewa Matsin Lamba Ba Zai Taba Raunana Al’ummar Iran Ba