8 Yuni 2020 - 06:07
Iran Ta Bayyana Alhininta Kan Rasuwar Sakataren Kungiyar Jihadul-Islami

Kasar Iran Ta Bayyana Alhininta Kan Rasuwar Tsohon Babban Sakataren Kungiyar Jihadul-Islami Ta Palasdinu

(ABNA24.com) A sakon ta’aziyarsa kan rasuwar tsohon babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami Ramadan Abdullahi Shalah da ya rasu a jiya Asabar: Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana mamacin da cewa: Mutum ne mai kaunar ci gaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan al’ummar Palasdinu da taimaka mata a gwagwarmayar neman ‘yanci.

Jawad Zarif ya bayyana tsananin bakin ciki da alhininsa kan rasuwar Dr Ramadan Abdullahi Shalah tsohon babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Palasdinu bayan shafe tsawon shekaru yana gudanar da gwagwarmayar neman ‘yancin Palasdinawa da Masallacin Qudus mai alfarma.

Zarif ya kara da cewa: Marigayi Dr Ramadan mutum ne mai kishin kasa kuma dan gwagwarmaya da ya jure dukkanin wahalhalu da kuncin rayuwa tare da sadaukar da ransa ta hanyar fuskantar duk wani hatsari da barazana domin yakar bakar zaluncin gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya ‘yan kaka gida.

A yammacin jiya Asabar ne tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihadul-Islami Dr Ramadan Abdullah Shalah ya rasu bayan fama da cutar ajali na tsawon lokaci, Allah ya jikansa da rahama tare da kyautata bayansa.


/129