(ABNA24.com) A ci gaba da gudanar da zanga-zangar da al’ummomin kasar Amurka suke domin nuna adawa da wariya bayan kisan bakar fata George Floyd da ‘yan sanda suka yi, a jiya an gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Washington fadar mulkin kasar ta Amurka.
Rahotanni daga birnin na Washington sun bayyana cewa, dubban mutane ne suka shiga cikin zanga-zangar, inda suka yi ta rera taken cewa; rayuwar baken fata tana da muhimmanci, tare da daga hotonan George Floyd.
Tun kafin wannan lokacin dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kirayi ma’aikatar tsaron kasar da ta jibge sojoji domin tunkarar masu zanga-zangar, wadanda ya kira da barayi ‘yan ta’adda.
Yanzu haka dai an shiga mako na biyu ana gudanar da wannan zanga-zanga ta miliyoyin jama’a a birane daban-daban na kasar Amurka, a daidai lokacin da ake kara samun baraka a tsakanin jami’an gwamnatin kasar kan irin matakan da gwamnatin Trump take dauka kan masu gudanar da wannan jerin gwano.
Baya ga kasar Amurka, an gudanar da irin wannan zanga-zanga a jiya a manyan biranan kasashen duniya daban-daban, da hakan ya hada da birnin London na Burtaniya, Sydney na Australia, Vienna na kasar Austria da sauransu.
/129
7 Yuni 2020 - 09:24
Lambar labari: 1044147
A ci gaba da gudanar da zanga-zangar da al’ummomin kasar Amurka suke domin nuna adawa da wariya bayan kisan bakar fata George Floyd da ‘yan sanda suka yi, a jiya an gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Washington fadar mulkin kasar ta Amurka.