(ABNA24.com) A cikin wani bayani da ya rubuta a shafinsa na twitter, Admiral Ali Shamkhani ya bayyana cewa, shugaban kasar Amurka Donald Trump yana cikin wani mawuyacin hali na gaba kura baya Siyaki, inda bai gama kubuta daga kura-kuran da ya tafka kan batun corona ba, sai kuma ga batun zanga-zangar al’ummar kasar kan ta nuna adawa wariya.
Ya ce shugaban na Amurka na kokarin samo wata hanya ta lallabar Iran domin ya samu wani karfin gwiwa wanda zai taimaka masa wajen cimma manufofinsa na siyasa, Shamkahani ya ce babu wani batun tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.
Bayan musayar fursunonin da aka yi tsakanin Amurka da Iran, a jiya Trump ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga tattaunawa tare da Iran, domin kulla manyan yarjeniyoyi tsakanin Iran da Amurka, kiran da ke ci gaba da shan martani daga bangarori daban-daban na manyan jami’an gwamnatin kasar ta Iran.
/129
7 Yuni 2020 - 09:24
Lambar labari: 1044140
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani ya bayyana cewa, babu tattaunawa tsakanin kasarsa da Amurka.