(ABNA24.com) Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana wariyar da wasu suke nuna wa bakaken fata a Amurka da cewa abin kunya ne da Allawadai, tare da yin kira da a hukunta makasa George Floyd.
Tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya mayar da kakkausan martani ci gaba da nuna wa bakaken fata wariya a kasar Amurka, inda ya ce wannan bai kamata ya faru a cikin 2020 ba, domin kuwa ya kamata ne a ce an wuce lokacin.
Barack Obama ya ce; abin bakin ciki da takaici ne, yadda har yanzu wasu miliyoyi daga cikin Amurkawa suna fuskantar matsalar nuna musu banbanci a cikin kasarsu, wanda hakan wani nau’i ne na dabbanci da hauka.
Ya ce yana kira da babbar murya ga mahukunta jihar Minnesota, da su dauki matakai na yin hukunci na adalci a kan wadanda suka aikata laifin kisa da ganganci, kuma bisa wariya ta launin fata, a kan George Floyd, domin yin hakan ita kadai ce hanyar shawo kan halin da kasar ta shiga a yanzu, sakaakon wannan kisa.
/129
31 Mayu 2020 - 07:56
Lambar labari: 1041874
Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana wariyar da wasu suke nuna wa bakaken fata a Amurka da cewa abin kunya ne da Allawadai, tare da yin kira da a hukunta makasa George Floyd.