28 Mayu 2020 - 05:07
Gwamnatin Rasha Ta Musanta Zargin Ta Aika Sojoji Zuwa Kasar Libya

Vladimir Janarouf dan majalisar dattawan kasar Rasha ya musanta zargin da ke cewa kasarsa ta aike da sojoji zuwa kasar Libya don taimakawa mayakan Halifa Haftar wadanda suke iko da gabacin kasar, a yakin da suke fafatawa da gwamnatin hadin kan kasar.

(ABNA24.com) Vladimir Janarouf dan majalisar dattawan kasar Rasha ya musanta zargin da ke cewa kasarsa ta aike da sojoji zuwa kasar Libya don taimakawa mayakan Halifa Haftar wadanda suke iko da gabacin kasar, a yakin da suke fafatawa da gwamnatin hadin kan kasar.

Kamfanin dillancin labaran Interfax na kasar Rasha ya nakalto Janarouf yana fadar haka a wata tattaunawa da ta hada shi da tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta zargi Rasha da shigar da sojoji cikin kasar ta Libya don taimakawa mayakan Halifa haftar.

Har’ila yau kwamandan sojojin Amurka a nahiyar Afirka AFRICOM ya sake nana wannan zargin daga ba ya, ba tare da gabatar da wani dalili ba. Sannan tare da rufe ido dangane da shishigin da Amurka take yi a cikin lamuran kasashen Afrika ta rundunar ta Africom.

Tun bayan kifar da gwamnatin Mu’ammar Kazzafi tsohon shugaban kasar Libya wanda ‘yan tawayen kasar suka yi tare da taimakon kasashen yamma a shekara ta 2011 ne, kasar ta kasa samun kwanciyar Hanklai har zuwa yanzu.


/129