(ABNA24.com) A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, daya daga cikin manufofin Iran mafi muhimmanci shi ne kara bunkasa alaka da kyayyawar danganta da kasashen nahiyar Afirka.
Ya ce wannan na cikin siyasar kasarsa, kuma har kullum dangantaka tsakaninsu za ta ci gaba a dukkanin bangarori. Haka nan kuma ya mika sakon taya murna ga dukkanin takwarorinsa na kasashen Afirka, kan zagayowar ranar Afirka, wadda ta kama jiya 25 ga watan Mayu.
Wannan rana dai ta yi daidai ne da ranar da shugabannin kasashaen Afrika 30 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa kungiyar hada kan kasashen Afrika wacce ake kira OAU a takaice a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia shekaru 57 da suka gabata.
Shuabannin kasashen Ghana, Masar da kuma Guinea na lokacin ne suka yi ruwa suka yi tsaki wajen kafa wannan kungiyar. Sai kuma a watan Yuli na shekara ta 2002 kungiyar ta zama tarayyar Afirka wato AU.
/129
26 Mayu 2020 - 06:54
Lambar labari: 1040121
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, ya mika sakon taya murnar zagayowar ranar Afirka ta duniya.