(ABNA24.com) A watan Aprilun da ya gabata fadar white Hause ta dakatar da kukaden da take bawa hukumar ta WHO bayan da ta zargeta da karkata zuwa ga kasar China, da kuma nuna rashin iya aiki wajen tunkarar Annobar korona Virus .
A wata wasika da shugaban na Amurka ya aikewa da shugaban hukumar ta WHO Adhnom Ghebreyesus ya fadi cewa a fili yake kurakuren da hukumar ku take ta maimaitawa wajen tunkarar cutar Annobar Korona da ta mamaye duniya ya sa biyan farashi mai tsada, don haka hanya daya tilo da hukumar za ta ci gaba shi ne ta kwaci yancita daga kasar China,
Yace a duk shekara Amurka na biyan hukumar kudi $ miliyan 450 amma ba ta yi mana abin da ya dace ba , ta bamu shawarwari marasa kyau , don haka za su yanke dukkan kudaden da suke ba ta idan basu ga wani canji ba.
/129
20 Mayu 2020 - 07:42
Lambar labari: 1038624
Shugaban na Amurka ya fadi cewa Amurka za ta fice daga hukumar lafiya ta duniya matukar bata sauya halayyartaba, na zama yar Koran kasar China, ya ci gaba da cewa akwai yiwu war ta dakatar da dukkan tallafin da take bawa hukumar har a abada, matukar ba a ga wani sauyi na a zo a gani ba,