17 Mayu 2020 - 08:00
Sudan Ta Musanta Cewa Tana Shirin Maida Hulda Da Isra'ila

Minista, mai bada shawara a ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ya bayyana cewa gwamnatin rikon kwaryar kasar ba ta da wani shiri na maida huldar jakadancin da haramtacciyar kasar Isara'ila (HKI).

(ABNA24.com) Minista, mai bada shawara a ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ya bayyana cewa gwamnatin rikon kwaryar kasar ba ta da wani shiri na maida huldar jakadancin da haramtacciyar kasar Isara'ila (HKI).

Kamfanin dillancin labaran Spotnic ya nakalto Ali Qamaruddeen yana fadar haka, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar ba za ta amince ta maida huldar jakadanci da HKI ba don yin hakan zai jawo mata matsaloli masu yawa da wasu kasashen yankin.

Kafin haka dai shugaban majalisar gudanarwa na gwamnatin kasar ta Sudan Abdulfattah Alburhan ya gana da firai ministan HKI Benyamin Natanyahu a birnin Kampala na kasar Uganda a farkon watan Fabrairun da ya gabata. AlBurhan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ce ta shirya haduwarsa da Natanyahu a kasar Uganda.

Bayan ganawar dai firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya wallafa wani rubutu a shafinsa na twitter inda ya bayyana cewa Isra’ila ta kama hanyar maida huda da kasar Sudan .

Kungiyoyi masu zaman kansu da kuma jam’iyyun siyasar a kasar ta Sudan dai sun yi ta zanga-zangar kin amincewa da duk wata hulda da HKI.


/129