(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar hadaddiyar daular larabawa Abdullah Bin Zaid Al Nahyan ya bayyana shirin Isra’ila na hade yankunan Falastinawa da yankunan da ke karkashin ikonta da cewa, hakan ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.
Tashar Almayedeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ya fitar, ministan harkokin wajen UAE Abdullah Bin Zaid Al Nahyan ya ce; shirin Isra’ila na kwace yankunan Falastina a gabar yamma da kogin Jordan tare da hade su da sauran yankunan da ke karkahsin Isra’ila, ba abu ne da kasarsa za ta amince da shi ba.
Ya ce ko shakka babu hakan zai rusa dukkanin kokarin da aka yi na ganin an samu nasarar kafa kasashe biyu masu cin gishin kansu, wanda kuma shi kadai ne hanyar samun zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falastinawa.
Kafin wannan lokacin ma dai kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta kirayi wani zaman gaggawa kan wanann batu, inda ta jaddada rashin amincewarta da hakan.
Gwamnatin kasar Amurka ce dai ta bayar da dama ga Isra’ila, kan ta kwace yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, domin ta gade su da sauran yankunan da ke karkshin ikonta.
/129
12 Mayu 2020 - 08:05
Lambar labari: 1036033
Ministan harkokin wajen kasar hadaddiyar daular larabawa Abdullah Bin Zaid Al Nahyan ya bayyana shirin Isra’ila na hade yankunan Falastinawa da yankunan da ke karkashin ikonta da cewa, hakan ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.