(ABNA24.com) Rahotanni daga birnin Kasla na kasar Sudan na cewa, kura ta lafa a birnin biyo bayan tashe-tashen hankula na kabilanci da suka auku a cikin wannan mako wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, hukumomin kasar Sudan sun bayar da bayanin cewa, a halin yanzu kura ta lafa a birnin Kasla da ke tazarar kilo mita 800 a gabashin birnin Khartum, biyo bayan rikicin kabilancin da ya barke a garin a cikin wannan mako.
Gwamnan lardin na Kasla Babakar Hamad ya bayyana cewa, a halin yanzu an shawo kan rikicin da ya faru na kabilanci a tsakanin kabilun Bani Amir da kuma Nauba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane daga dukkanin kabilun biyu.
A nasa bangaren shugaban majalisar shugabancin kasar Sudan Abdulfattah Burhan ya bayyana takaicinsa matuka dangane da abin da ya faru, tare da kiran al'ummar Sudan zuwa ga hadin kai da fahimtar juna da kuma zaman lafiya.
Ko a ranar Laraba ta gabata ma an kashe kimanin mutane 30 a wani rikicin na kabilanci a yankin Darfur da ke yammacin kasar ta Sudan.
/129
12 Mayu 2020 - 07:57
Lambar labari: 1036015
Rahotanni daga birnin Kasla na kasar Sudan na cewa, kura ta lafa a birnin biyo bayan tashe-tashen hankula na kabilanci da suka auku a cikin wannan mako wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane.