6 Mayu 2020 - 08:17
Dakarun Sa-Kai Na “Hashdu-Sha’abi” Na Kasar Iraki Sun Rusa sansanin Kungiyar Da’esh

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto majiyar kafar labarai ta “Bagdad al-Yaum’ tana cewa; Mayakan sa –kai na Irakin, sun kai wa sansanin Da’esh da ke gabashin gundumar Salah hari, lamarin da ya haddasa tashin gobara a cikin sansanin.

Ehlibeyt (as) Haber Ajansı ABNA - Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto majiyar kafar labarai ta “Bagdad al-Yaum’ tana cewa; Mayakan sa –kai na Irakin, sun kai wa sansanin Da’esh da ke gabashin gundumar Salah hari, lamarin da ya haddasa tashin gobara a cikin sansanin.

Har ila yau, dakarun sa-kan, na “Hashd” sun kuma kai wa wasu hare-haren akan mabuyar ‘yan ta’addar a gundumar “Mikshifah’ inda su ka lalata ta baki daya.

Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai gyauron kungiyar ta “Da’esh” su ka kai wasu hare-hare akan cibiyoyin jami’an tsaron Iraki da dakarun sa kai na “Hashd” tare da kashe wasu ga cikinsu.

Wadannan hare-haren dai suna zuwa ne a daidai lokacin da ake kai gwauro da mari a kokarin kafa sabuwar gwamnati a kasar.



/129