4 Mayu 2020 - 03:41
​Iran: Ba Za A Gudanar Da Jerin Gwanon Ranar Quds Ta Duniya Ba

Kwamitin da ke kula da shirya tarukan ranar Quds ta duniya a kasar Iran ya sanar da cewa, ba za a gudanar da jerin gwanon ranar Quds ta duniya a wannan shekara ba saboda annobar corona.

(ABNA24.com) Tashar Al-alam daga birnin Tehran ta bayar da rahoton cewa, a zaman da aka gudanar yau tsakanin mambobin kwamitin da ke shirya tarukan ranar Quds, da wakilai daga ma’aikatun harkokin waje, cikin gida, kiwon lafiya, da kuma dakarun IRGC, an cimma matsaya kan cewa ba za a gudanar da jerin gwanon ranar Quds ba.

Kakakin kwamitin Ramadan Sharif ya sanar da cewa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki na bullar cutar corona a wannan lokaci, an dakatar da gudanar da duk wani jerin gwano na ranar Quds a fadin kasar ta Iran, amma a maimakon hakan za a raya wannan ranar ta wasu hanyoyi na daban.

Ana gudanar da jerin gwamnon ranar Quds ta duniya a Juma’ar karshe a kowane watan Ramadan, domin nun a goyon baya ga al’ummar musulmi na Falastinu da suke fuskantar zalunci da mamaya daga yahudawan Sahyuniya.




/129