4 Mayu 2020 - 03:41
​Masar: Sojoji Sun Ce Sun Halaka 'Yan Ta'adda 126 A Arewacin Sinai

Rundunar sojin kasar Masar ta sanar da halaka 'yan ta'addan takfiriyya 126 a yankin arewacin Sinai.

(ABNA24.com) Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da rundunar sojin kasar Masar ta sanar a yau, ta bayyana cewa; dakarun kasar sun kaddamar da wani babban farmaki a Sinai, wanda ya yi sanadiyyar halaka 'yan ta'addan takfir 126.

Bayanin ya ce an kaddamar da wannan farmaki ne da nufin ci gaba da tsarkake yankin daga 'yan ta'adda, wadanda suke yin barazana ga tsaron kasar da al'ummarta, inda aka kame wasu 266 daga cikin wadanda ake nema, sai kuma sojoji 15 da suka rasa rayukansu.

Kafin wannan lokacin da 'yan sa'oi, ma'aikatar harkokin cikin gida akasar ta Masar ta sanar da kashe wasu 18 a garin Bi'irul Abd, bayan musayar wuta da aka yi tsakaninsu da jami'an tsaro.



/129