28 Afirilu 2020 - 04:52
Fiye Da Mutane 40 Ne Su Ka Mutu Saboda Fadace-fadace A Gabashin Kasar DRC

Kamfanin dillancin labarun AFP ya ambato cewa kwanadi hudu da aka dauka ana fada a gabashin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 43.

(ABNA24.com) Majiyar sojan kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo wacce ta sanar da hakan, ta kara da cewa; A ranar Juma’a ne wasu mahara dauke da wukake da bindigogi su ka kshe fararen hula 21 a yankin Mahagi a gundumar Ituri.

Bugu da kari a kusa da yankin Djugu ma an sami barkewar wani fadan a jiya Lahadi a tsakanin sojojin gwamnati da kuma wasu masu dauke da makamai a garin Lisey.

Kakakin soja a yankin Laftanar Jules Ngongo ne ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP haka, yana mai kara da cewa; A yayin fadan an kashe sojoji biyu da kuma wasu fararen hula guda biyu.

Sai dai sojojin sun yi nasarar kashe maharan su 12.

A ranar Lahadin da ta gabata ma kungiyar ADF ta kai hari a gundumar Kivu ta Arewa, inda ta kashe mutane shida.

Wani rahoto na MDD ya ce daga 2017 zuwa yanzu an kashe fiye da mutane 700 a yankin na Ituri saboda fadace-fadace.


/129