(ABNA24.com) Da marecen yau Litinin ne dai mataimakin shugaban kasar ta Iran Sattari ya ce; A lokacin da ake shiga matsi ne ake yin kirkire-kirkire,a wannan yanayin na matsalar corona da aka shiga mun samar da kayan da mu ke fitar da su zuwa kasashen waje.
Daga cikin kayayyakin da Iran din ta kera wadanda kuma ta wadata da su a cikin gida, sannan ta fara fitar da su zuwa waje, sun kunshi; Na’urar auna zafin jiki da kayan da ake amfani da su a cikin dakunan bayar da kulawa ta musamman ga marasa lafiya, suna daga cikin abubuwan da Iran ta ke kerawa tun kafin bullar cutar corona.
Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa tuni an cimma yarjejeniya da ma’aikatar kiwon lafiya domin fara fitar da kayan zuwa waje.
/129
28 Afirilu 2020 - 04:52
Lambar labari: 1030735
Mataimakin Shugaban kasar Iran akan ilimi da fasaha ne ya bayyana cewa kasar za ta fara fitar da kayan gwajin corona da ta kera zuwa kasar waje.