26 Afirilu 2020 - 06:15
Jagora Ya Jaddada Muhimmancin Habaka Koyar Da Al’kur’ani Mai Girma Da Kuma Tafsirinsa

Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamnei wanda ya ke mayar da jawabi na wata wasika da malamin al’kur’ani mai girma a Iran, Muhsin Kara’ati ya aike masa, ya bayyana cewa; “ Hakika Allah madaukakin sarki ya ba ku samun dace a wannan fage, muna kuma rokonsa akan ya kara mu ku wannan dacen.

(ABNA24.com) Ayatullahil-Uzma Sayyid Ali Khamnei wanda ya ke mayar da jawabi na wata wasika da malamin al’kur’ani mai girma a Iran, Muhsin Kara’ati ya aike masa, ya bayyana cewa; “ Hakika Allah madaukakin sarki ya ba ku samun dace a wannan fage, muna kuma rokonsa akan ya kara mu ku wannan dacen.

Jagoran ya kuma kara da cewa; Na amince da muhimmancin yin aiki tukuru wajen bunkasa koyar da al’kur’ani mai girma da kuma tafsirinsa.

Hujjatul Islam Muhsim Qara’ati ya aike wa da jagoran juyin musuluncin na Iran wasika da a ciki yake karfafa wajabcin a sake zage damtse wajen bunkasa da yada karatun al’kur’ani mai girma da tafsirinsa, haka nan kuma hukunce-hukuncen fikihun da su ke cikinsa.


/129