26 Afirilu 2020 - 06:15
 An Kaddamar Da Shirin Samar Da Allurar Riga kafi Da Ta Maganin Covid-19

Majalisar dinkin duniya, da hukumar lafiya ta duniya, da wasu manyan kasashe gami da cibiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa, sun kaddamar da shirin samar da allurar rigakafi da kuma maganin warkar da cutar covid-19 da ta addabi duniya.

(ABNA24.com) Majalisar dinkin duniya, da hukumar lafiya ta duniya, da wasu manyan kasashe gami da cibiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa, sun kaddamar da shirin samar da allurar rigakafi da kuma maganin warkar da cutar covid-19 da ta addabi duniya.

Shugaban hukumar lafiya WHO Tedros Adhnom Ghebreyesus, wanda ke gabatar da jawabin kaddamar da wannan shiri, ya ce Za a yi kokari domin samar da wannan allurar rigakafi duk da cewa aikin zai iya daukar dogon lokaci kafin a kai ga samun nasara.

Babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya ce maganin zai shafi kowa da kowa ba tare da nuna bambanci ba tsakanin talaka ko mai kudi.

Mista Guteres ya yi kiran kasashen duniya su jingine siyasa domin samar da maganin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan cuta ya doshi dubu 200 a wannan Asabar.



/129