26 Afirilu 2020 - 06:15
Yau Ta Ke Ranar Yaki Da Zazzabin Malaria

Yau 25 ga watan Afrilu, ita ce ranar da hukumar lafiya ta duniya ta ware domin yaki da zazzabin cizon sauro cewa da malaria.

(ABNA24.com) Yau 25 ga watan Afrilu, ita ce ranar da hukumar lafiya ta duniya ta ware domin yaki da zazzabin cizon sauro cewa da malaria.

Sai dai bikin ranar na bana ya zo ne a daidai lokacin da hankulan duniya suka karkata wajen yaki da cutar Coronavirus.

Kafin hakan dama hukumar ta WHO, ta yi gargadin kada a manta da matakan da ake dauka na yaki da cutar a daidai wannan lokaci da duniya ke fama da cutar corona.

Masana kiwon lafiya na da fargabar za’a iya fuskantar karancin kudi don yaki da wannan zazzabin na malaria, lura da yadda karfin duniya ya koma kacaukam ga batun yaki da Covid-19.

A shekarar 2018, sama da mutane miliyan 228 ne suka yi fama da wannan zazzabi, inda dubu 405 suka rasa rayukasu, to sai dai hukumar lafiya ta duniya ta ce adadin wadanda za su mutu a bana zai iya kaiwa dubu 700 mafi yawansu a Afirka.




/129