(ABNA24.com) A kasar Chadi, mutane 44 ne da ake tsare da bisa zargin alaka da kungiyar boko haram suka rasa rayukansu a wani gidan yarin kasar.
Babban mai shigar da kara na kasar ta Chadi, Youssouf Tom, ya ce an gano gawarwakin ne a ranar Alhamis da safe.
A cewar M.tom, tuni aka binne 44 daga cikinsu, hudu kuma daga cikinsu wadanda aka kai asibiti, bincike ya nuna cewa sun sha wata guda ce wacce ta haifar masu da matsalar zuciya, wasu kuma ta haifar masu da masananciyar matsalar numfashi.
Fursunonin dai na daga cikin mutane 58 da aka cafke yayin farmakin da sojojin Chadin suka kaddamar kan ‘yan boko haram a yankin tafkin Chadi a makwannin da suka gabata.
Ministan shari’a na kasar ta Chadi ya bayyana wa kamfanin dilancin labaren france Press cewa an kaddamar da bincike kan lamarin, tare da yin watsi da jita jitan cewa an muzgunawa mutanen ne, ta hnayar hana su abinci da ruwa tun bayan mayar dasu N'Djamena, babban birnin kasar.
/129
20 Afirilu 2020 - 06:32
Lambar labari: 1027639
A kasar Chadi, mutane 44 ne da ake tsare da bisa zargin alaka da kungiyar boko haram suka rasa rayukansu a wani gidan yarin kasar.