19 Afirilu 2020 - 06:32
​Muhammad Salah Ya Aike Da Taimakon Abinci Da Kayan Yaki Da Corona A Masar

Shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Masar da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Livepool a kasar Burtaniya, ya bayar da taimakon abinci ga mabukata a wasu yankuna na Masar.

(ABNA24.com) Shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Masar da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Livepool a kasar Burtaniya, ya bayar da taimakon abinci ga mabukata a wasu yankuna na Masar.

Jaridar Yaum Sabi ta kasar Masar ta bayar da rahoton cewa, Muhammad Salah ya aike da tan-tan na buhunnan abinci zuwa yankuna na kasar Masar, musammana mahaifarsa da ke Bisyun, domin a raba ga talakawa mabukata.

Baya ga abinci, Muhammad Salah ya taimaka da wasu daga cikin kayayyakin bukatar rayuwa da jama’a suke bukata, da kuma wasu da suka shafi kiwon lafiya, musamman na kare kai daga kamuwa da corona.

Muhammad Salah kan gudanar da ayyukan agaji ga al’ummar kasar Masar musamman marassa galihu daga cikinsu, inda yake bayyana hakan a matsayin daya daga cikin ayyuka na wajibi a kansa.



/129