(ABNA24.com) Jakadan hukumar ta ‘yan gudun hijira a Tehran Ivo Freijsen ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake hira da kamfanin dillancin labaran “Iran Press” na kasar Iran a nan birnin Tehran a jiya Asabar.
Jakadan ya kara da cewa hukumarsa za ta hada kai da wadanda abin ya shafa don ganin an tallafawa kasar Iran dangane da kula da ‘yan gudun hijira na kasar ta Afghanistan da suke kasar.
Har’ila yau Jakadan ya jinjina wa Jagoran juyin juya halin musulunci Ayat. Sayyeed Aliyul Khamine’i wanda ya bayar da umurnin na ilmantar da ‘yan gudun hijirar kasar ta Afghanistan a makarantun gwamnatin kasar kyauta.
Gwamnatin kasar Iran dai tana kashe dalar Amurka biliyan $8 kan ‘yan gudun hijirar Afghanistan a kowace shekara.
/129