14 Afirilu 2020 - 05:53
​Jaridar Turkiya Ta Fitar Da Bayanai A Kisan Khashoggi

Jaridar Sabah ta kasar Turkiya, ta fitar da wasu bayanai dangane da kisan dan jaridar kasar Saudiyya Jamal Khashoggi, da ke nuna da cewa Muhammad Bin Salman na da hannu kai tsaye a cikin lamarin.

(ABNA24.com) Jaridar Sabah ta kasar Turkiya, ta fitar da wasu bayanai dangane da kisan dan jaridar kasar Saudiyya Jamal Khashoggi, da ke nuna da cewa Muhammad Bin Salman na da hannu kai tsaye a cikin lamarin.

Jaridar ta bayyana cewa, bisa ga bayanan da bangaren shari’a na kasar Turkiya ya tattara kan kisan Jamal Khashoggi, dalilai da dama suna nuni da cewa yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Muhammad Bin Salman ne ke da hannu kai tsaye wajen bayar da umarnin kisan.

Daga cikin abubuwan da aka dogara da su kuwa akwai manyan na hannun damarsa wadanda suke cikin lamarin dumu-dumu, daga ciki kuwa hard a wanda ya shirya kisan baki daya Saud Qahtani, wanda shi ne babban na hannun damar Bin Salman, wanda ya fi kowa kusa da shi.

Baya ga haka kuma sautin da aka nada ta wasu hanyoyi a lokacin da aka kashe Jamal Khashoggi a cikin ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Istanbul, da kuma kalaman da makasan suka rikayi a lokacin, wanda ke danganta lamarin kai tsaye da Bin Salman.

Haka nan kuma wani bayanin daya daga cikin makasan, wanda ya yi jim kadan bayan kammala kisan Khashoggi, wanda yake isar da wannan sako ga na Qahtani domin sanar da Bin Salman.


/129