1 Afirilu 2020 - 10:16
Coronavirus Ta Hallaka Amurkawa 865 A Rana Guda

Shugaba Donald Trump, na Amurka, ya bayyana cewa makwanni biyu masu zuwa zasu kasance masu matukar bakin ciki ga kasar.

(ABNA24.com) Trump, ya bayyana a taron manema labarai daga fadar White House cewa, zamu fusknaci makwanni biyu masu matukar wahala.

Kalamman na Trump, na zuwa ne a daidai lokacin da adadin mamata da masu kamuwa da cutar coronavirus ke ci gaba da karuwa a kasar.

A alkalumman baya baya nan da aka fitar mutum 865 ne suka rasa rayukansu sanadin cutar, wanda kuma shi ne adadi mafi yawa da aka samu a kasar kawo yanzu tun bayan bullatar.

A Amurka dai Trump, na ci gaba da shan suka akan yadda tunda farko ya yi wa al’amarin cutar ta coronavirus rikon sakainar kashi.

342