(ABNA24.com) A cikin sanarwar da ta fitar, hukumar ta NCDC ta bayyana cewa, an samu karin mutane 11 da suka kamu da cutar coronavirus a cikin Najeriya, inda adadin masu dauke da cutar ya haura daga 70 zuwa 81 a halin yanzu.
Hukumar ta ce mutane 8 daga cikin mutane 11 da suka kamu da cutar daga jihar Legas ne, biyu kuma daga Enugu, daya kuma da jihar Edo.
Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana daukar dukkanin matakan da suka dace domin dakile yaduwar wannan cuta a fadin kasar, kamar yadda a nasu bangaren, gwamnatocin jihohin kasar su ma suna daukar nasu matakan kan hakan.
Najeriya dai ita ce kasar da tafi yawan al’umma a dukkanin nahiyar Afrika, kuma cutar ta shigo kasar ne ko dai ta hanyar ‘yan kasashen turai da suka shigo kasar, ko kuma ‘yan Najeriya da suka yi tafiya zuwa turai suka shigo da ita, daga ciki kuwa har da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar.
/129
29 Maris 2020 - 08:24
Lambar labari: 1021426
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa a Najeriya (NCDC) ta sanar da cewa, an kara samun wasu mutane 11 da suke dauke da cutar corona a kasar.