21 Maris 2020 - 10:43
​Kamfanoni 20 A Duniya Suna Aiki Tukuru Domin Samar Da Riga Kafin Corono Virus

Hukumar lafiya ta duniya ta bada sanarwan cewa masana a wurare daban-daban a duniya suna aiki tukuru don samar da rigakafi ga cutar nan

(ABNA24.com) ta Corona Virus. Tashar talabijin ta CNBC ta nakalto Maria Van shugaban bangaren taimakon gaggawa na hukumar ta Lafiya yana cewa, a halin yanzu masana a kasashe akalla 20 sun dukufa wajen gano rigakafin wannan cutar. Sannan ya kara da cewa wannan abin farin ciki ne da gaske, sai dai ya ce za’a dau lokaci kafin wannan riga kafin ya isa hannu kowa da kowa.

CNBC ta nakalto Van yana fadin haka a wani taron ‘yan jarida da ya kira a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa hukumar ba za ta amince da rigakafin da ba’a dau lokacin da ya dace a dauka ana gwada shi ba, don duk maganin da za’a yiwa mutane da dama ya kamata a yi taka tsatsan wajen amincewa da shi da sauri.

Van ya ce abinda ya fi Corona Virus hatsari shi ne mummunan rigakafi, wanda ba’a tabbatar da ingancinsa ba.

Ya zuwa yanzu dai Corona Virus ta kashe mutane 276,104 a duniya, wanda 10,442 daga cikinsu sun mutu sai kuma mutane 91,952 sun warke daga cutar.

342