(ABNA24.com) sanarwan cewa ma’aikatar ta sami nasarar kubutar da wani ba’iraniye mai suna
Jalal Ruhullahi-Najad daga inda ake tsare da shi a kasar Faransa da nufin mika
shi ga kasar Amurka.
Ghulam –Husain Isma’ila ya bayyana haka ne a jiya Juma’a ya kuma kara da cewa an kama Ruhullahi-Najad ne a shekarar da ta gabata a wata tashar jiragen sama a kasar Faransa tare da umurnin kasar Amurka.
Amurka tana tuhumar Jalal Ruhullahi-Najad da sabawa takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar Iran. Don haka ne wata kotu a kasar ta Faransa ta yanke hukuncin a mika shi ga ma’aikatar shari’a ta kasar Amurka. Wannan hukuncin ya sami amincewar ma’aikatar shari’ar kasar ta Faransa.
Amma tare da kokarin ma’aikatar shari’a na kasar Iran Faransa ta amince a yi musayarsa da wani dan kasar ta Faransa wanda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 5 a nan kasar Iran.
342