14 Maris 2020 - 06:00
Iran Ta Aike Wa MDD Wasikar Bukatar A Cire Mata Takunkumi Domin Yakar Coronavirus

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif, ya aike wa babban sakataren MDD, wata wasika, wacce a ciki ya bukaci a soke takunkuman zaluncin da Amurka ta kakaba wa kasar, ta yadda Iran din za ta samu damar yaki da cutar numfashi ta coronavirus.

(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif, ya aike wa babban sakataren MDD, wata wasika, wacce a ciki ya bukaci a soke takunkuman zaluncin da Amurka ta kakaba wa kasar, ta yadda Iran din za ta samu damar yaki da cutar numfashi ta coronavirus.

Da ya ke sanar da hakan a shafinsa na Twitter, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Seyed Abbas Moussavi, ya ce Dakta Zarif, ya aike wa sakatare janar na MDD, da wasikar a ranar Alhamis 12 ga wata, inda ya bukaci a cire dukkan jerin haramtatun takunkuman na Amurka kan Iran domin ta samu sukunin yaki da cutar coronavirus.

Haka zalika kuma a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ya ce an aike da irin wannan wasika ga shugabannin kungiyoyin kasa da kasa da kuma ministocin harkokin waje na dukkan kasashe.

Tun dai bayan bullar cutar ta Covid-19 a Iran, yanzu haka ta kashe mutane 429 a fadin kasar. 



/129