14 Maris 2020 - 06:00
​Iraki: Amurka Ta Kai Hare-Hare Kan Sansanonin Hashdu Al-sha'abi

Sojojin Amurka a kasar Iraqi sun kai hare-hare kan wurare da dama malakin dakarun sa kai na kasar Iraqi wacce ake kira “Hashdushabi” inda suka kasha mutane da dama.

(ABNA24.com) Sojojin Amurka a kasar Iraqi sun kai hare-hare kan wurare da dama malakin dakarun sa kai na kasar Iraqi wacce ake kira “Hashdushabi” inda suka kasha mutane da dama.

Majiyar ma’aikatar cikin gida na kasar Iraqi ta bada sanarwan cewa da misalign karfe 01.15 na dare jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare kan sansanin mayakan da ke Jurf al-Nasr kilomita 60 daga birnin Bagdaza, da kuma Musayyib a cikin lardin Babil, kusa da hubbaren Imam Aliyu (a) da ke birnin Najaf da kuma wani harin a kan tsohon garin Alexandaria.

Labarin ya kaa da cewa sakataren tsaron kasar Amurka . Mark Esper, ya tabbatar da kai wadannan hare-hare a ma’aikatar Pentagon amma bai fadi yawan mutanen da suka kasha ba.

Har’ila yau a wani labarin jami’an gwamnatin kasar ta Iraqi sun tabbatar da cewa sojojin Amurkan sun kai hari kan wani filan sauka da tashin jiragen sama kilomita 100 daga birnin Karbala inda hubaren Imam Husain (a) jikan manzon All..(s) yake.

Tashar talabijin ta CNN a Amurka ta nakalto Jami’an Pentagon na cewa sun kai hare-haren ne kan rumbunan ajiye makamai na dakarun sa kai din ne.



/129