(ABNA24.com) Rahoton ya bayyana cewa Muhammad Bin Salman yarima mai jiran gadon masarautar kasar ta Saudiyya, ya bayar da umarnin kame ‘ya’yan gidan sarautar ne bisa zarginsu da yake yi da yunkrin juyin mulki a kasar.
Kamar yadda ya zo a cikin wannan rahoto, daga cikin wadanda aka kame akwai Ahmad bin Abdulaziz dan uwa shakiki ga sarkin kasar Salman Bin Abdulaziz, kamar yadda kuma aka kame dansa Naif bin Ahmad bin Abdulaziz, sai kuma Muhammad Bin Naif tsohon yarima mai jiran gado, da kuma Nawaf bin Naif dan uwansa shakiki.
Kafin wannan lokacin dai a ranar Asabar da ta gabata, jaridar ta wall Street Journal ta bayar da rahoton kame yarima Ahmad Bin Abdulaziz dan uwa shakiki ga sarki Salman, da kuma Muhammad bin Naif, tsohon yarima mai jiran gado, da kuma dan uwansa Nawaf bin Naif, amma cikin kasa da kawana guda, Muhammad Bin Salman ya bayar da umarnin kame karin wasu daga cikin 'ya'yan gidan sarautar kasar.
Wannan mataki na zuwa ne bisa ga abin da uke gani cewa, Muhammad Bin Salman na kokarin ganin bayan duk wani mai karfin fada a ji a cikin iyalan Al Saud, domin kada su kawo masa cikas ga yunkurinsa na darewa kan kujerarar sarautar kasar ta Saudiyya bayan mutuwar sarki salman, ko kuma kafin mutuwarsa.
Haka nan kuma irin wannan matakin zai iya shafar ‘yan jarida masu tasiri a kasar, kamar yadda ya shafi Jamal Khashoggi sakamakon sukar salon mulkin Yarima Muhammad Bin Salman.
/129
10 Maris 2020 - 10:48
Lambar labari: 1016254
Jaridar The Middleast ta bayar da bayanin cewa ya zuwa yanzu ‘ya’yan gidan sarautar Saudiyya 20 ne Muhammad Bin Salman ya bayar da umarni aka kame su.