10 Maris 2020 - 10:34
An Halaka Sojojin Amurka Biyu A Kasar Iraki

Ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta Pentagon ta sanar da halakar jami’anta sojojinta guda biyu a kasar Iraki.

(ABNA24.com) Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta bada rahoton cewa, a jiya Litinin ne ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta Pentagon ta bada sanarwan halaka sojojin na ta arewacin kasar ta Iraki.

Bayanin ya ce an halaka sojojin ne da suke yin aiki tare da sojojin kasar ta Iraki a matsayin ma su bayar da shawara kan yaki da ‘yan ta’adda na kungiyar Daesh a arewacin kasar, kuma wasu makiya kasar Amurka ne suka kashe su.

Ma’aikatar tsaron kasar ta Amurka ta boye sunayen mutanen biyu, bisa abin da ta kira bukatar yin haka daga iyalansu, wadanda bisa dokar dokar Amurka dole ne a mutunta bukatarsu.

Da dama daga cikin mutanen kasar Iraki dai sun yi imanin kan cewa, Amurka ba da gaske take ba, dangane da yaki da ‘yan ta’addan ta Daesh a kasar, a yayin da wasu suke ganin cewa tana taimaka ma ‘yan ta’adda ne, ta hanyoyi daban-daban a cikin kasar ta Iraki.



/129