(ABNA24.com) A yammacin jiya Shugaban kasar Aljeriya Abdulmajid Tabun ya gana da sarkin Qatar Tamim Bin Hamd Al thani a fadarsa da ke birnin Aljiers babban birnin kasar.
Bangarorin biyu sun tattauna kan alaka da ke tsakaninsu da kuma yadda za su kara bunkasa ta, kamar yadda kuma suka tattauna a kan batutuwa da suka shafi yankin gabas ta tsakiya da ma batutuwa na kasa da kasa.
Har’iala yau bangarorin biyu sun jaddada wajabcin warware batun kasar Falastinu da aka mamaye ta hanya mafi adalci, wadda za ta baiwa Falastinawa hakkokinsu da aka haramta musu, tare da jaddada wajabcin yin aiki tare a tsakanin dukkanin kasashen larabawa da na musulmi domin ganin an kawo karshen mawuyacin halin da al’ummar Falastinu tace ciki tsawon shekaru fiye da 70.
Tun a ranar Litinin da ta gabata ce dai sarkin an Qatar ya fara gudanar da ziyarar aiki a kasar Tunisia, inda ya gana da shugaban kasar da sauran manyan jami’an kasar.
/129