(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dar Hassan Ruhani ya bayyana cewa Imam Khomeini (q) wanda ya kafa JMI ya bukaci mutane su fito don zaben wanda suka ga dama a matsayin shuwagabanninsu. Shugaban ya bayyana haka ne a yau Lahadi a lokacinda ya kai ziyarar jaddada bai’a a kabarin marigayi Imam Khomeini da ke kudancin birnin Tehran.
Shugaban ya mika sakon taya murna ga al’ummar kasar dangane da zagayowar ranar da Imam Khomeini ya dawo daga gudun hijira a ranar 1 ga watan Fabrairu na 1979.
Dr Hassan Ruhani ya ce, ko shakka babu za su ci gaba da tafiya a kan tafarkin marigayi Imam Khomeini (q) da kuma hannunka mai sanda na jagoran juyin musulunci Ayatulah Sayyid Ali Khamenei domin kai wa ga manufofin juyin.
Shugaba Rauhani ya kuma jinjinawa dukkanin wadanda suka rasa rayukansu, ta hanyar sadaukarwa domin cimma manufa ta koli ta wannan juyin, haka nan kuma da wadanda suka ci gaba da yin riko da wannan tafarkin har zuwa yanzu.
/129
3 Faburairu 2020 - 06:11
Lambar labari: 1007370
Shugaban kasar Iran Dar Hassan Ruhani ya bayyana cewa Imam Khomeini (q) wanda ya kafa JMI ya bukaci mutane su fito don zaben wanda suka ga dama a matsayin shuwagabanninsu. Shugaban ya bayyana haka ne a yau Lahadi a lokacinda ya kai ziyarar jaddada bai’a a kabarin marigayi Imam Khomeini da ke kudancin birnin Tehran.