1 Faburairu 2020 - 10:48
​Burtaniya Ta Fice Daga Kungiyar Tarayyar Turai A Hukumance

Kasar Burtaniya ta fice daga cikin mambobin kungiyar ta​Burtaniya Ta Fice Daga Kungiyar Tarayyar Turai A Hukumancerayyar turai a hukumance.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa,a daren jiya ne gwamnatin kasar Burtaniya ta sanar da cewa ta fice daga cikin kungiyar tarayyar turai, tare da bayyana ranar a matsayin ta tarihi a kasar.

Firayi ministan kasar ta Burtaniya Boris Johnson ya bayyana cewa, tsawon shekarun da kasar ta dauka a cikin kungiyar tarayyar turai ba ta iya cimma abubuwan da take bukata ba, amma yanzu za su aiki tukuru domin ganin ci gaban kasar.

‘Yan sa’oi bayan wannan sanarwa, an saukar da dukkanin tutocin Burtaniya a dukkanin cibiyoyi na kungiyar tarayyar turai da ke birnin Brussels na Belgium fadar mulkin tarayyar turai.

Bayan wannan sanarwa dubban masu goyon bayan ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar turai sun bazama kan tituna a biranan kasar, kamar yadda kuma a daya bangaren dubban masu adawa da ficewar kasar su ma suka fito a kan tituna a fadin kasar.




/129