Taskar watsa ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito Ministan harkokin wajen kasar Iran, Mohammad Javad Zarif, ya bukaci shugaba Donald Trump na Amurka, ya rika aiki da hujjoji ba wai kannun labaren tashar talabijin ta Fox News ba.
Haka kuma a cewar Mista Zarif, shugaban kasar ta Amurka ya bai dogoro da faci-fadi na mashawarta ko kuma masu fasara masa farisanci, ya rika daukan matakai akan hujjoji.
A daya bangaren kuma lokacin da yake amsa tambaya jaridar ‘’ Der Spiegel’’ ta Jamus, ta cewa ko Iran za ta tattaunawa da Amurka, ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya ce ba zamu kauda yiyuwar tattaunawa da Amurka ba, amma da sharadin gwamnatin Trump, ta sauya tunaninta kan Iran da kuma dagewa Iran din jerin takunmumai.
A game da batun yiyuwar ko MDD ta dawo da takunkuman kan Iran, Mista Zarif, ya amsa cewa ai tuni shugaban kasar ta Iran Hassan Rohani ya bayyana matakan da Iran din za ta dauka a cikin wata wasika da ya aike wa bangarorin da suka sanya wa yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran hannu, a don haka a cewarsa kasashen turan ne zasu girbi martanin da Iran za ta dauka.