Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ABNA24- ta rawaito cewa; Da dama daga cikin kafofin yada labarai sun fi mayar da hankali kan batun da ya yin a cewa, martanin da Iran ta mayarwa Amurka tare da rugurguza sansanin sojin Amurka a Iraki, ya zubar da Amurka a idon duniya.
Haka nan kuma yadda ya bayar da muhimmanci ga martanin da dakarun kare juyi suka mayar, inda ya ce ranar da suka mayar da martani ta zama daya daga cikin manyan ranaku masu muhimmanci a kasar.
Baya ga haka kuma kafofin yada labarai sun kawo batun da ya yin a fitowar miliyoyin jama’a a dukaknin biranan da aka gudanar da rakiyar janazar Qasim Sulaimani a Iran, inda ya ce wannan shi shi tabbatar da cewa al’ummar kasar suna tare da juyi, sabanin abin da kasashe masu adawa da kafofin yada labaransu suke ta hankoron nuna wa duniya.
Haka nan kuma wani batu mai matukar muhimmanci shi ne batun harbo jirgin fasinja bisa kure da ya auku, inda ya mika sakon ta’aziyyarsa ga dukkanin iyalan wadanda lamarin ya shafa
Dangane da batun makomar
yarejjeniyar nukiliya kuwa, ya bayyana matakin da kasashen turai suke shirin
dauka kan cewa Iran ta saba wa yarjejeniyar da cewa, abin da suke son su yi shi
ne tilasta Iran ta durkusa a kan gwiwarta, lamarin da Amurka ma ta kasa yin
hakan balantana su masu yi mata amshin shata.