Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}ABNA24- ta rawaito, Sayyid Abdulmalik Al Hutsis a cikin jawabinsa na bikin shekara-shekara na ranar shahidai, inda ya ke cewa; Bikin na shekarar bana ya zo ne a daidai lokacin da abubuwa masu muhimmanci su ke faruwa da raunana a duniya za su amfana da su.
Da ya juya akan Magana shahadar Qasim Suleimani da Abu Mahdi al-Muhandis, wadanda Amurka ta yi wa kisan gilla, Sayyid Abdulmalik al-Hutsis ya ce; Harin da Amurka ta kai wanda ya yi sanadiyyar shahadar musulmi biyu ta’addanci ne.