Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Jummaʼa

22 Nuwamba 2024

15:37:11
1506972

'Yan Shi'a 108 Su Kai Shahada Bayan Harin Da 'Yan Ta'addan Takfiriyya Su Kai A Pakistan

Adadin shahidan harin ta'addancin da aka kai wa 'yan Shi'a na Parachenar a Pakistan ya kai shahidai 108 / jarirai 12 ne suka yi shahada a harin takfiriyya + Bidiyoyi

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As ABNA ya habarta cewa: Shahidan harin ta'addancin da aka kai kan motoci dauke da 'yan Shi'ar Pakistan a kan hanyar Parachenar zuwa Peshawar sun kai shahidai 108.

Ɗaya daga cikin masu fafutukar yada labaran kasar Pakistan ya bayar da labarin faruwar wasu sabbin hare-haren laifukan ta'addanci da 'yan ta'addar takfiriyya suka kai wa 'yan shi'ar yankin "Parachenar" da ke kan hanyarsu daga birnin Parachenar zuwa Peshawar.

"Syed Ali Ahmar Zaidi" daya daga cikin masu fafutukar yada labaran Pakistan a wata hira da wakilin Abna dangane da girman wannan ta'addanci ya ce: adadin shahidan harin da 'yan takfiriyya suka kai kan wasu motocin safa bas a kan hanyar Parachenar zuwa Peshawar ya kai mutane 108 da suka hada da jarirai goma sha biyu kuma an jikkata wasu da dama a wannan ta'addancin. Wasu kuma adadin ‘yan Shi’a na Parachenar su ma sun bace a wannan harin, kuma babu labarinsu.

Ya kara da cewa: Bayan harin da 'yan takfiriyya suka kai, wasu mutane sun sauko daga cikin motocin bas, suka gudu don tsira da rayukansu, amma 'yan ta'addan suka bi su suka shahadantar da su. Har ma ‘yan ta’addan sun shiga gidajen da ‘yan Shi’a suka fake suka shahadantar da su.

Abun da ya kamata a sani shine cewa a Jiya ranar Alhamis 21 ga November, 2024, ayarin motocin da ke dauke da gungun 'yan Shi'ar Pakistan na tafiya daga Parachenar zuwa Peshawar, yayin da wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai musu hari. Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin na ta'addanci, amma kafin wannan harin 'yan Shi'ar Pakistan sun sha fuskantar hare-hare daga kungiyoyin takfiriyya irin su ISIS, Sipah Sahaba da Lashkar Jahangu a sassa daban-daban na kasar.