15 Yuli 2024 - 07:34
An Kama 'Yan Kungiyar ISIS Kafin Su Kai Hari A Wurin Zaman Makokin Ashura A Birnin Kabul

An dakile harin da kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta yi yunkurin kaiwa kan taron masu juyayin Ashura a babban birnin kasar Afganistan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na kasa da kasa na Ahlul Bayt (AS) - ABNA – ya kawo maku rahotan cewa:- Al-Mirsad, kafar yada labarai mai alaka da kungiyar Taliban ta sanar a cikin wani rahoto da ta fitar cewa, hukumomin leken asirin gwamnatin Taliban sun dakile tare da hana reshen Khurasan na kungiyar ta'addanci ta Da'ish aiwatar da wani harin su kai yunkurin kaiwa kan taron juyayin Ashura a Kabul, babban birnin kasar Afganistan.

Wannan Kamfanin labaran ya habarta cewa, wasu daga cikin ‘yan kungiyar ISIS sun shirya kai harin ta’addanci a wajen taron zaman makokin Ashura na birnin Kabul, amma ba su samu damar aiwatar da wannan farmaki ba inda asirinsu ya tonu.

Bisa wannan rahoton jami'an hukumar leken asirin gwamnatin Taliban sun ce kwanaki hudu da suka gabata sun lalata wata maboyar 'yan ta'addar ISIS a yanki na biyar na birnin Kabul.

A cikin rahoton na wannan kafar yada labarai da ke da alaka da Taliban, an kuma bayyana cewa an kama 'yan ta'addar Daesh, amma ba a tantance ko nawa aka kama daga cikin wadannan 'yan ta'adda ba.

Kafar yada labarai ta Al-Mirsad ta ruwaito cewa, wanda ke jagorantar maboyar da aka gano a birnin Kabul dan kasar Afghanistan ne, kuma reshen Khurasan na ISIS ya ba shi wannan aikin ta'addanci.

Da take tabbatar da rahoton kama tare da dakile yunkurin 'yan ta'addar ISIS a wannan birni, rundunar 'yan sandan Kabul ta sanar da kwace makamai da alburusai daga hannun 'yan ta'addar ISIS da aka kama a Kabul.

"Khalid Zardan" daya daga cikin jami'an tsaron gwamnatin Taliban a birnin Kabul ya bayyana cewa: An kama wasu 'yan ta'addar ISIS a sakamakon wani samame na musamman na jami'an leken asiri da aka yi tare da lalata maboyar 'yan ta'addar ISIS a wannan farmakin.

Kungiyar ISIS reshen Khurasan ta kai hare-haren ta'addanci da dama a kan masallatai da cibiyoyin mabiya Shi'a a biranen Kabul, Hirat da Baghlan a cikin shekarar da ta gabata.

An kama mayakan ISIS a birnin Kabul yayin da manyan jami'an Taliban a kodayaushe ke ikirarin cewa ISIS ba ta da samuwa a Afghanistan a cikin 'yan watannin nan.