Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hukumar Harkokin Fursunoni Falasdinawa da Kungiyar Fursunoni Falasdinawa sun bayyana a cikin wata sabuwar sanarwar hadin gwiwa da aka fitar a yau, Alhamis, cewa wadannan laifukan ta’addancin sun shafi dukkan fursunoni ba tare da togiya ba, ta hanyar manufofi da hanyoyin da aka tsara ta hanyar da ba a taba ganin irinta ba. Sun dauki abin da ke faruwa a matsayin muhimmin bangare na yakin kare dangi da kuma ayyukan "kawar da mulkin mallaka ke anfani da shi" da take ci gaba da yi kan al'ummar Falasdinawa.
Sanarwar ta dogara ne akan ziyarce-ziyarce da dama da aka gudanar a watan Disamba na 2025, wanda ya ƙunshi gidajen yari da cibiyoyin tsare mutane da dama, ciki har da gidajen yari na Ofer, Negev, Megiddo, da Ramle, da kuma sassan Rekefet, Shatta, Gilboa, da Ganot, ban da sansanonin tsare mutane, musamman Sde Teiman da Gilad.
Dangane da fursunoni mata, rahoton ya bayyana cewa fursunoni mata 50 da ke tsare a gidan yarin Damon an yi musu danniya da ta'addanci, ciki har da amfani da hayaki mai sa hawaye, duka, daure musu hannu, da kuma tilasta musu zama a cikin yanayi mai sanyi.
Haka kuma ya tabbatar da hana kayayyakin tsafta na mata na yau da kullum, da kuma hana kula da lafiya, har ma da fursunonin da ke fama da cututtuka na yau da kullun, ciki har da ciwon daji.
Rahoton ya nuna yanayin da ake ciki a gidan yarin Ganot, inda ake tsare da wasu shugabannin ƙungiyoyin fursunonin Falasɗinawa, ciki har da Sakatare Janar na Jam'iyyar 'Yantar da Falasɗinawa, Ahmad Sa'adat. Kungiyoyin biyu sun tabbatar da cewa ana tsare da waɗannan shugabannin a cikin mawuyacin hali, tare da ci gaba da azabtarwa, tsare su kaɗai, da hana su magani, wanda ya haifar da mummunan raunuka na jiki, gami da karyewar haƙarƙari da ciwon baya mai tsanani.
A gidajen yarin Gilboa da Shatta, rahoton ya nuna ƙaruwa sosai a yawan matakan danniyawa fursunoni, ciki har da amfani da duka, hayaki mai sa hawaye, da sanduna a kan fursunoni. Ya kuma ishara da ci gaba da "siyasar yunwa" a gidan yarin Nafha, inda ake ba wa fursunoni abinci dan fincini sau uku a rana, wanda ke haifar da raguwar nama da rage kiba, da kuma barkewar cututtukan fata kamar su scabies, da kuma kamuwa da wasu fursunoni da ƙwayoyin cuta waɗanda ba a san asalinsu ba ba tare da samun magani mai mahimmanci ba.
Sanarwar ta nuna kasancewar fursunoni sama da 1,400 daga Zirin Gaza da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, waɗanda aka bayyana a matsayin azabtarwa mai tsanani da kuma keta mutuncin ɗan adam. Ya kuma nuna cewa kimanin fursunonin yara 350 suna fuskantar mawuyacin hali, ciki har da hana ziyartar iyali da kula da lafiya, duka, da rashin abinci mai gina jiki. Kwamitin Harkokin Fursunoni na Falasdinu da Ƙungiyar Fursunoni ta Falasdinu sun kammala rahotonsu da jaddada cewa manufofin mamaya suna mayar da hankali kai tsaye kan ciin mutuncin fursunoni ta hanyar ci gaba da cin zarafi da wulaƙanta su, waɗanda ake gudanarwa a kowane lokaci a cikin gidajen yari.
..........
Your Comment