Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

12 Faburairu 2024

04:52:00
1436927

Sabon Harin Jiragen Yakin Sahyoniyawan A Rafah Yayi Sanadin Shahidar Fiye Da Mutane 100

Shahidan harin kisan kiyashin Rafah sun kai mutane 110. Firaministan yahudawan sahyoniya ya ci gaba da wuce gona da iri bayan hare-haren da suka faru a baya, ya bukaci lalle sai an kaiga rusa bataliyoyin soji na kungiyar Hamas a Rafah gabanin watan Ramadan.

Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na - ABNA -  ya bayar da rahoton cewa: majiyoyin yada labarai sun bayar da rahoton cewa, harin da ba a taba ganin irinsa ba da gwamnatin sahyoniya ta kai kan birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza yayi sanadin shahada da raunata daruruwan mutane.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, jiragen yakin Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai a gidaje da masallatai da dama a yankunan Rafah da ke dauke da yawan jama'a.

Majiyoyin lafiya sun bayyana cewa kimanin shahidai 110 da kuma wasu da dama da suka samu raunuka ne aka samu sakamakon harin da yahudawan sahyuniya suka kai kan gidaje 14 da masallatai 3 a Rafah.

A safiyar yau litinin an ji karar artabu da manyan bindigogi da kuma jiragen sama a birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza.

Dangane da haka, an samu labarin wani kazamin rikici a kusa da asibitin Kuwaiti Rafah.

Hare-haren da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai a Rafah na cikin wani yanayi da 'yan gudun hijira Palasdinawa sama da miliyan daya da rabi da suka tsere daga yankunan arewaci da tsakiyar Gaza suka samu mafaka a can.

A baya dai Isra'ila ta kira Rafah a matsayin daya daga cikin wuraren da Falasdinawa za su iya tserewa su samu mafaka.

A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama da kuma mambobin kasashen duniya sun yi gargadi game da duk wani farmakin da sojojin mamaya za su kai a Rafah.

A baya-bayan nan ne firaministan gwamnatin Sahayoniya Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa, za a fara kai farmaki ta kasa a Rafah nan da makonni 2 masu zuwa. Firaministan yahudawan sahyoniya ya ci gaba da wuce gona da iri bayan hare-haren da suka faru a baya, ya bukaci lalle sai an kaiga rusa bataliyoyin soji na kungiyar Hamas a Rafah gabanin watan Ramadan.

A sa'i daya kuma, tashar 12 ta gwamnatin Sahayoniya ta bayyana rashin jituwar da ke tsakanin Netanyahu da Herzi Halevi kan yiwuwar kai farmaki a Rafah.

Kafafen yada labaran sahyoniyawan "Kan" sun ruwaito a daren Asabar cewa, Amurka ta bukaci Isra'ila da ta kaurace wa hare-haren soji da kuma kai hare-hare a Rafah, musamman a wannan wata na Ramadan.