Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Manufar wannan shiri dai ita ce raunana karfin gwagwarmaya da suka hada da Iran, Hizbullah, Hamas, kungiyoyin gwagwarmaya na Iraki, da kuma Ansarullah na kasar Yemen.
A kasar Labanon, majalisar ministocin kasar, sakamakon matsin lamba daga wakilin Amurka na musamman Thomas Barak, ta yi watsi da ra'ayin bangarorin al'ummar ƙasar ba, kuma a yayin da babu ministocin Shi'a (Hizbullah da kungiyar Amal), sun amince da shirin kwance damarar Hizbullah a taronta na ranar 5 ga watan Agusta.
Wannan mataki na majalisar ministocin Lebanon ya fuskanci martani daga jam'iyyun Shi'a na kasar. Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem, ya yi kakkausar suka ga gwamnatin kasar Labanon a jawabinsa na taron Arbaeen na Imam Husaini (AS) a birnin Baalbek a ranar Juma'a tare da nuna adawa da matakin da ta dauka na baya-bayan nan.
Your Comment