30 Agusta 2025 - 21:25
Source: ABNA24
Yamen: Mun Sha Alwashin Ɗaukar Fansa Ga Harin Isra'ila 

Daga cikin wadanda su kai shahada akwai Firayim Minista, da Ministan Yada Labarai, Ministan Lafiya, Ministan noma, Ministan Harkokin Waje, Ministan Shari'a, Ministan Tattalin Arziki, da Sakataren Gwamnatin Yaman a wannan harin.

Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Shugaban Majalisar Koli ta Siyasa ta Yemen: Mun sha alwashin daukar fansa. Makiya maciya amana sun kawo mana wannan harin ta'addancin, amma mun sha alwashin tare da izinin Allah, al'ummar Yaman maɗaukaka, da iyalan shahidai da wadanda suka jikkata, cewa za mu dauki fansa da gina nasara daga zurfafan raunukan.

Za mu ci gaba, kuma ba za ku sake dandana tsaro ba daga yau.

Daga cikin wadanda su kai shahada akwai Firayim Minista, da Ministan Yada Labarai, Ministan Lafiya, Ministan noma, Ministan Harkokin Waje, Ministan Shari'a, Ministan Tattalin Arziki, da Sakataren Gwamnatin Yaman a wannan harin.

Baya ga Sanarwar shahadar da dama daga cikin ministocin gwamnatin Yaman.

Hizbullah Ta Labanon Ta Jajantawa Gwamnatin Yemen.

Bayan sanar da shahadar firayim minista kuma ministan yada labarai na kasar Yaman, Ansarullah ta tabbatar da shahadar wasu ministocin kasar a harin da yahudawan sahyuniya suka kai birnin San'a na baya bayan nan.

Hizbullah a cikin wata sanarwa da ta fitar ta sanar da cewa: Muna mika ta'aziyyarmu da juyayi ga 'yan'uwanmu 'yan kasar Yemen da kuma jagoransu, karkashin jagorancin Sayyid Abdul Malik Badreddin al-Houthi, dangane da shahadar Mujahid Ahmed Ghalib al-Rahwi, firaministan gwamnatin canji da gyara tare da wasu gungun ministocin kasar, sakamakon harin da 'yan ta'addar Sahayoniyya suka yi a kan taron da bana tsaro ba na Gwamnatin Yemen a Sana'a babban birnin kasar.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha