Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbay (As) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya tabbatar da cewa gwamnatin kasar Labanon ta dauki wani mataki mai hatsari a ranar 5 ga watan Agusta, wanda ya saba wa zaman tare, yana mai gargadin cewa, hakan na iya jefa kasar cikin mawuyacin hali.
Ya kamata a lura da cewa a wannan rana, firaministan kasar Labanon Nawaf Salam ya sanar, bayan zaman majalisar ministocin kasar da ya tattauna batun "takaita makamai", cewa ya dora wa sojojin kasar alhakin samar da wani shiri na aiwatarwa game da "kayyade makamai ga kasar" kafin karshen shekara tare da mika shi ga majalisar ministocin kasar don tattaunawa, ba daga baya ba fiye da 31 ga Agusta.
Gwamnatin Labanon Ita Ke Da Alhakin Duk Wani Rikici Na Cikin Gida Na Labanon.
A jawabin da ya gabatar a wajen taron tunawa da Imam Husaini As na Arbaeen a birnin Baalbek, Sheikh Qassem ya ce gwamnatin kasar Labanon ta dauki wani mataki mai hatsarin gaske tare da keta haddin zaman tare, yana mai gargadin cewa tana yunkurin jefa kasar cikin mawuyacin hali. Ya dorawa gwamnatin alhakin duk wani rikici na cikin gida da kuma watsi da aikinta na kare kasar Lebanon.
Ya kara da cewa, "Ba ma son fitina, amma akwai masu yin aiki don haifar da ita".
Gwamnatin Lebanon Tana Hidima Ga Shirin Isra'ila Da Amurka
Sheikh Qassem ya yi nuni da cewa, gwamnatin Lebanon tana aiwatar da umarnin Amurka da Isra'ila ne domin kawo karshen gwagwarmaya, ko da kuwa hakan zai haifar da yakin basasa da kuma rikicin cikin gida.
Ya ce, wannan gwamnati tana yi wa Isra’ila aiki ne da hidima, ko ta sani ko ba ta sani ba.
Ya yi jawabin, yana mai cewa, "Idan kun ji ba za ku iya ba, ku bar abokan gaba su tunkare mu, kamar yadda yake-yaken Isra'ila da suka ci gaba da yi bai ci nasara ba, to a wannan karon za ta sha kaye".
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya yi kira da "ka da a saka sojoji cikin rikicin cikin gida, saboda tarihinsu ba shi da tabo, kuma shugabancinsu ba ya son shiga cikin wannan tafarki".
Lebanon Ba Ta Da Rayuwa Idan Kun Tsaya A Bangare Daya
Ya kara da cewa, "Mu kasance tare wajen gina kasar, ba za a gina kasar da wani bangare ba tare da wani ba, za mu zauna tare cikin mutunci, ko kuma Lebanon ba za ta samu rayuwa ba idan kun tsaya a daya bangaren".
Shehin malamin ya jaddada: "aikin gwamnati ba shine ta mika kasar ga makiya da kuma ta'addancin Amurka ba." Ya ce, "Ta yaya a cikin gwamnati za ku yarda ku sauƙaƙe kashe abokan aikinku a cikin gida? Shin Lebanon za ta tsira idan wasu abokanta a cikin gida suka far wa wasu?" Ya kara da cewa, "Shin kun ji shirin Netanyahu na kafa 'Babban Isra'ila'? Menene ra'ayinku?" Me kuke yi?
Gwagwarmaya Ba Za Ta Mika Makamanta Ba Yayin Da Ake Ci Gaba Da Kai Hare-Hare.
Ya ce, Gwagwarmaya ta samu halaccinta ne daga jinin shahidai, kuma ba ta bukatar hallacci daga gare ku, ina gaya muku, kada ku saka sojojin Lebanon cikin rikicin cikin gida.
Sheikh Qassem ya jaddada cewa Gwagwarmaya ba za ta mika makamanta ba yayin da ake ci gaba da kai hare-hare kuma ana ci gaba da mamayewa, za mu yi yaki irin na Karbala idan bukatar hakan ta taso, kuma muna da yakinin cewa za mu yi nasara.
Ya kara da cewa, "Mun sha fadin cewa, ku dakatar da ta'addanci da keta iyaka, ku kori Isra'ila daga Lebanon". Za mu samar muku da dukkan kayan aiki yayin tattaunawa kan tsaro na kasa da dabaru".
Gwagwarmaya Bata Buƙatar Shaida Daga Wani.
Ya nanata cewa "Gwagwarmaya tana ba da shaida kuma bata buƙatar shaida daga wani". yana mai cewa "babban ra'ayin jama’ar Labanon yana tare da Gwagwarmaya da ci gaban ta".
Sheikh Qassem ya ce, "Ba za mu iya magana game da ikon shugabantar kasar Labanon ba, sai da goyn bayan gwagwarmayar da ta 'yantar da kasar ba".
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ya yi nuni da cewa, Gwagwarmaya ta taimaka wa gwamnatin kasar wajen karbe ikon kudancin Lebanon. Tsawon watanni takwas, ana ta kai hari ga Gwagwarmaya, duk da haka mun kasance da haƙuri.
Nasarar Yuli 2006 Nasara Ce Ta Azama Da Gwagwarmaya.
Sheikh Qassem ya yi ta'aziyya ga shahidan sojojin Lebanon da suka yi shahada a Zebqin, shahidan aiki da gaskiya, shahidan gwagwarmaya, sojoji, da al'umma.
Ya kara tunawa da yakin Yuli, yana mai cewa, "A yau muna gina rayuwarmu, makomarmu, da kuma tsararrakinmu a kan cewa kowace kasa da lokaci don nasara ne, bayarwa, sadaukarwa, da kuma cimma manyan manufofinmu".
Ya jaddada cewa "Nasarar da muka samu a watan Yulin 2006 nasara ce ta azama da tsayin daka, shan kaye ne ga Isra'ila, da kuma dakile ayyukan mamaya da matsugunan ta." Ya ishara da cewa wannan nasarar “ta kasance a matsayin koma baya ga Isra’ilawa tsawon shekaru 17”.
Kisan Kare Dangi Ba Zai Sa Falasdinawa Su Karaya Daga Gwagwarmaya Ba.
Daga nan sai ya gode wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa goyon bayan da take ba wa gwagwarmaya da kudi da makamai da mukaman siyasa da sadaukarwar shahidai.
Ya jaddada cewa Falasdinu za ta ci gaba da zama mataimaka, kuma kisan kiyashi ba zai sa al'ummar Palasdinu su ja baya da gwagwarmaya ba.
Ya ce, "Falasdinu za ta yi nasara duk da irin wannan sadaukarwa, domin su ne ma'abota kasa, manufa, azama, da jinni da sadaukarwa".
......
Your Comment