30 Agusta 2025 - 20:58
Source: ABNA24
Yamen: Firaminista Da Wasu Gungun Ministoci Sun Yi Shahada A Harin Da Isra'ila Ta Kai

Firaministan Yaman da wasu gungun ministoci sun yi shahada tare da jikkata wasu a harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai a Sanaa.

Kamfanin Dillancin Labarain ƙasa da ƙasa Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cikin wata sanarwa da ofishin firaministan gwamnatin kasar Yemen mai kula da harkokin a birnin Sanaa ya fitar ya sanar da shahadar firaministan kasar tare da wasu gungun ministoci a harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai a ranar Alhamis din da ta gabata.

Sanarwar ta ce: Muna sanar da shahadar Mujahid "Ahmad Ghalib Al-Rahwi", Firayim Minista na gwamnatin canji da yin gyara, tare da wasu ministocin da ke tare da shi, a harin da Isra'ila ta kai a ranar Alhamis din da ta gabata. A wannan harin an kuma raunata wasu ministoci da dama wadanda wasunsu ke da matsakaicin raunata wasu kuma sun samu munanan raunuka kuma ana sa ido da kulawa da su.

Ministan yada labaran kasar Yaman yana ɗaya daga cikin wadanda su kai yi shahada a hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai a baya-bayan nan

Hashem Sharafuddin ministan yada labaran kasar Yemen ya yi shahada a harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai birnin Sanaa a ranar Alhamis din da ta gabata.

A wannan babban laifin ta'addanci da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai hari kan taron majalisar ministocin kasar Yemen da munanan hare-haren ya ta kai ga shahadar firayim minista Ahmed Ghalib Al-Rahwi da wasu ministocin gwamnatin kasar.

Your Comment

You are replying to: .
captcha