26 Disamba 2019 - 06:44
Sabuwar Zanga - zangar Fada Da Tsadar Rayuwa Ta Barke A Kasar Sudan.

Daruruwan Al’ummar kasar Sudan ne suka sake fitowa akan tituna domin gudanar da Zanga- zangar nuna adawar da matsanancin halin tattalin arziki da suke ciki, inda suka bukaci gwamnatin Hadaka a kasar da ta cika alkawuran da ta dauka na warware matsalar tattalin arziki da suke ciki.

(ABNA24.com) Daruruwan Al’ummar kasar Sudan ne suka sake fitowa akan tituna domin gudanar da Zanga- zangar nuna adawar da matsanancin halin tattalin arziki da suke ciki, inda suka bukaci gwamnatin Hadaka a kasar da ta cika alkawuran da ta dauka na warware matsalar tattalin arziki da suke ciki.

Wannan Zanga - zanga tana zuwa ne ‘yan sa’oi bayan shugaban gwamnatin hadakar kasar Abdallah Hamduk ya fara bayani game da cika shekara 1 da zagayowar Zanga-zangar gama gari a da akayi a kasar da ta kai ga ture tsohuwar gwamnatin Umar Albashir, inda mutane suka sake bayyana a gaban fadar shugban kasar da ke birnin Khartum dauke da tutocin kasar da hotunun wadanda aka kashe a tarzomar baya bayan nan, inda suka yi kira da a kawo karshen matsalar tattalin arziki da ta da bai baye kasar.

Kwamitin likitoci kasar Sudan ya yi ikirarin cewa daga lokacin da aka fara Zanga- zangar neman sauyi a watan Disamba shekarar da ta gabata a kasar zuwa yanzu kimanin mutane 246 suka kwanta dama, yayin da sama da 1300 kuma suka jikkata. Sai dai ma’aikatar lafiya ta kasar ta nuna cewa adadin wadanda suka kwanta dama 1804 ne.

Zanga- zangar neman sau yi da aka yi ne ta kifar da gwamnatin Albashir kuma ta kawo gwamnatin rikon kwarya a ranar 21 ga watan Ogusta da aka sanya cewa acikin watanni 39 za’a samar da yanayin da zai bada damar gudanar da zabe da kuma mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula.




/129